12
1 Da shike muna kewaye da wannan irin kasaitaccen taro na shaidu, sai mu watsar da dukkan abubuwan dake nawaita mana da kuma zunubin da zai saurin makale ma na. Bari a cikin hakuri mu yi tseren da ke gabanmu.
2 Bari mu kafa idonmu ga Yesu, wanda shine mafarin bangaskiyarmu da cikarta. Wanda sabili da murnar da a ka sa a gabansa ya jimre giciye, ya kuma yi watsi da kunyarsa, wanda kuma ya zauna a hannun dama na kursiyin Allah.
3 Ku dube shi wanda ya jimre irin wannan adawa daga masu zunubi, domin kada ku gaji ko ku karai.
4 Ba ku yi tsayayya ko jayayya da zunubi har ta kai ga zub da jininku ba tukunna. Kun kuma manta da gargadin da a ka yi maku a matsayin 'ya'ya:
5 ''Dana, kada ka dauki horon Ubangiji da wasa, kadda kuma ka yi suwu lokacin da ka sami horonsa,''
6 Domin kuwa Ubangiji yana horon dukkan wadanda yake kauna, yana kuma hukunta duk wadanda ya karba.
7 Ku daure wahala a matsayin horo. Allah yana yi da ku kamar 'ya'yansa, domin kuwa wanne da ne wanda ubansa bazai yi masa horo ba?
8 Amma idan baku da horo kamar yadda sauran mutane ke da shi, kun zama shegu kenan ba 'ya'ya ba.
9 Hakannan kuma kamar yadda muke da iyaye a duniya wadanda suke yi mana horo, kuma muna basu daraja. To ba sai mu yiwa Ubanmu na Ruhaniya biyayya don mu rayu ba?
10 Ta wani fanni kuwa iyayenmu suna yi mana horo na kwanaki kadan bisa ga yadda suka ga ya dace, Amma Allah kuwa yana yi mana horo domin anfanin kanmu, domin kuma mu sami rabo daga cikin tsarkinsa.
11 Ba horon da ke da dadi a lokacin yinsa, amma sai zafi. Sai dai kuma bayan haka yakan haifar da 'ya'ya na ruhaniya da kuma adalci ga dukkan wadanda aka yi rainonsu a ciki.
12 Don haka sai ku karfafa hannayenku da ke reto, da kuma guwawunku da ke kaduwa.
13 Ku bi hanyoyi mikakku domin abin da ya gurgunce kada ya karye amma ya warke.
14 Ku bidi salama da kowa, da kuma rayuwar tsarki wanda in ba tare da shi, babu wanda zai ga Allah.
15 Ku mai da hankali domin kada waninku ya rasa, alherin Allah, kuma kada wani tushe mai daci ya tsiro a cikinku har ya haifar da fitina, domin kada da dama daga cikinku su gurbata ta wurinsa.
16 Ku yi hankali kuma kada a sami mazinanci ko marar ibada a cikinku, kamar Isuwa, wanda sabili da abinci ya sayar da 'yancinsa na dan fari.
17 Kun kuwa san cewa sa'adda ya yi marmarin ya gaji albarka a gaba, an kishi, domin kuwa bai sami damar tuba ba, ko da shike ya nema har da hawaye.
18 Domin kuwa baku zo ga dusen da ake tabawa da hannu ba, dutse ne mai ci da wuta, da tukuki da bakin hayaki da hadari.
19 Ba Ku zo ga karar kaho mai ban razana da murya mai firgitarwa ba, da masu sauraro suka yi roko kar su sake jinta.
20 Don basu iya jimre abin da aka yi doka a kan saba: ''koma dabba ce ta taba dutsen, sai a jejjefe ta.''
21 Abin tsoro ne kuwa kwarai, har Musa yace, ''A tsoroce nake kwarai har na firgita.''
22 Maimakon haka kun zone ga Dutsen Sihiyona da kuma birni na Allah mai Rai, kuma na Urushalima ta Samniya, da kuma dubun dubban mala'iku cikin murna da farin ciki.
23 Kun zo taro na dukkan 'ya'yan fari, rubuttatu a sama, kuma kun zo ga Allah wanda shine alkalin dukka, hakannan kuma zuwa ga ruhu na adalai wanda a ka rigaya aka tsarkake.
24 Kun zo ga Yesu, wanda shine matsakancin sabon alkawari, kuma ga jinin yayyafawa da ke magana fiye da na jinin Habila.
25 Ku yi lura kada ku ki wannan da ke yi mu ku magana. Gama in har basu kubuta yayin da su ka yi jayayya da wanda ya yi mu su gargadi a duniya ba, balle ma mu ba za mu kubuta ba in mun ki wanda ke mana gargadi daga sama.
26 A wani karo, muryar sa ta girgiza duniya. Amma yanzu yayi alkawari da cewa, ''Har'ila yau ba duniyar kadai zan girgiza ba, amma har da sammai.''
27 Wannan kalma, ''Harl'ila yau,'' ta bayyana cirewar abubuwan nan da za su girgizu, wato abubuwan da a ka halitta, domin abubuwan da ba zasu girgizu ba su kasance.
28 Don haka, samun mulkin da ba za ya girgizu ba, sai mu zama masu godiya, kuma a cikin wannan yanayi mu yi wa Allah sujada cikin daraja da tsaninin gimamawa.
29 Domin kuwa Allahnmu wuta ne mai konewa.