7
1 Wannan ne Malkisadak, sarkin Salem, firist na Allah Madaukaki, wanda ya gamu da Ibrahim na dawowa daga yaki da wasu sarakuna ya kuma albarkace shi.
2 Ibrahim ya ba shi ushirin dukkan ganimar da ya samu. Sunansa,” Malkisadak,” ma'anar itace, “Sarkin adalci,” haka ma, “sarkin salem,” ma'anar iitace,” Sarkin salama,”
3 Bashi da uwa bashi da uba, ba shi da lissafin asalin zuriya, ba shi da farkon rayuwa ba shi da karshen rai. Shi firist ne na har abada, kamar Dan Allah.
4 Yanzu fa dubi irin girman wannan mutum. Kakan kakanninmu Ibrahim ya bada ushira ta abubuwan da ya samo na ganimar yaki gare shi.
5 Kuma hakika, zuriyar Lawi da suka karbi aikin nan na firistanci suna da umarni daga shari'ar Allah cewa su karbi zakka a gun jama'a, wato, daga yan'uwan su Isra'ilawa, koda shike suma zuriyar Ibrahim ne.
6 Amma Malkisadak, shi da ba zuriyar Lawi ba ne, ya karbi zakka daga Ibrahim, ya kuma albarkace shi, shi wanda ya ke da alkawarai.
7 Ba jayayya, karami shi ke karban albarka daga babba wanda ya girme shi.
8 A wannan tsarin mutanen da ke karban zakka wata rana sai ka ga sun mutu, amma a wani kauli mutumin da ya karbi zakka a wurin Ibrahim, ance, wanzaje ne har yau.
9 Kuma bisa ka'ida Lawi, wanda ke karban zakka, shi ma ya bada zakka ga Ibrahim,
10 Saboda kuwa Lawi na cikin tsatson Ibrahim lokacin da Malkisadak ya gamu da Ibrahim.
11 Yanzu in da mai yiwuwa ne a sami kammala cikin aikin firistanci na Lawiyawa (domin ta wurin ta ne aka bada shari'a), to ina amfanin wani firist ya zo bisa ga ka'ida irin ta Malkisadak, ba'a kuma ambaci ka'idar Haruna ba?
12 Don kuwa lokacin da aka canza firistanci, shari'a kuma dole ne a sauya ta.
13 Domin mutumin da aka fadi wadannan abubuwa a kansa na wata kabila ne, wadda ba wani mutumin da ya taba yin aiki a kan bagadi.
14 Wannan a bayyane yake Ubangijinmu ya zo ne daga zuriyar Yahuza, kabilar da Musa bai taba anbatonsu game da zancen firistanci ba.
15 Abinda muke fadi a bayyane yake cewa, idan wani firist ya taso da kamanin Malkisadak.
16 Wannan sabon firist, ba firist ne da ya taso bisa ga ka'idar zuriya ta yan'adam ba, amma ya zama firist ne ta rayuwa mai iko marar shudewa.
17 Domin a rubuce yake cikin littafi ga me da shi; “Kai firist ne na har'abada bisa ga tsari irin na Malkisadak.”
18 Domin doka ta fari an ajiye ta a gefe guda saboda rarrauna ce kuma marar amfani.
19 Don kuwa shari'a ba ta iya kamalta kome. Amma fa a kwai bege mai kyau a nan gaba wanda ta gare shi ne zamu sami iso a gun Allah.
20 Kuma wannan kyakkyawan bege baya faruwa ba tare da rantsuwa ba, don kuwa su wadancan firistocin ba su dauki wata rantsuwa ba.
21 Amma Allah yayi rantsuwa game da Yesu cewa, “Ubangiji ya rantse ba kuwa zai fasa tunaninsa ba; 'Kai firist ne har'abada.'”
22 Ta wurin haka Yesu ya bada tabbatacce da kuma ingataccen alkwari.
23 Hakika, mutuwa ta hana firistoci su yi aiki har'abada. Wannan shi ya sa akwai firistoci da yawa daya bayan daya.
24 Amma da shi ke Yesu na rayuwa ne har'abada, aikinsa na firist ba a musanya shi sam sam.
25 Domin haka kuma yana da cikakken ikon ceton wadanda ke gusowa ga Allah ta wurinsa, domin kullum a raye ya ke yana kuma roko dominsu
26 . Domin irin wannan babban firist shi ne ya dace da mu. Ba shi da zunubi, marar abin zargi, tsarkakakke, kebabbe daga masu zunubi, ya na sama da sammai dukka.
27 Ba shi da bukata, kamar manyan firistoci, da ke mika hadayu kullum, da farko don zunubin kansu, sa'annan don zunubin jama'a dukka. Amma Yesu yayi wannan sau daya tak ba kari don kowa da kowa, yayin da ya mika kansa.
28 Domin shari'a na nada mutane da ke da gazawa a matsayin firistoci, amma maganar rantsuwa, wadda ta zo a bayan shari'a, ta nada Dan, wanda ya ke cikakke har'abada.