Yahuda
1
1 Yahuza, bawan Yesu Almasihu kuma dan'uwan Yakubu, zuwa ga kirayayyu, kaunatattu a cikin Allah Uba, kebabbu domin Yesu Kristi:
2 bari jinkai da salama da kauna su ribabanya a gare ku.
3 Kaunatattu, ina iyakar kokari in rubuta maku game da ceton mu duka, ya zama dole in gargade ku sosai game da bangaskiya wadda aka mika wa masu bi sau daya tak ba kari.
4 Don wasu mutane sun sadado sun shigo da sanda a asirce wadanda an rubuta game da hukuncin su tun da dadewa-mutane marasa imani, wanda suka canza alherin Allah zuwa lalata, kuma sun karyata makadaicin Shugaba da Ubangijinmu, Yesu Almasihu.
5 Ina so in tunashe ku-ko da shike kun rigaya kun san abin, da cewa Allah ya ceci wasu mutane daga kasar masar, amma daga baya ya hallaka wadanda basu ba da gaskiya ba.
6 Kuma mala'iku wadanda ba su rike matsayin ikon su ba, amma suka bar wurin zaman su na ainihi-Allah ya tsare su a sarka na har'abada a cikin bakin duhu domin babban ranar shari'a.
7 Suna nan kamar Saduma da Gwamrata da kuma biranen da ke kewaye da su, wadanda suka ba da kansu ga fasikanci suna bin sha'awoyi wanda ba na dabi'a ba. Aka mai da su abin misalin wadanda suka sha wuta mara matuka.
8 Haka kuma, wadannan masu mafarkan suna lalatar da jikinsu. Suna raina masu mulki, kuma suna fadar miyagun abubuwa a kan masu daukaka.
9 Amma ko Mika'ilu babban mala'ika, a lokacin da yake jayyaya da muhawara da shaidan a kan gawar Musa, bai kuskura ya fadi wata kalmar hukunci a kansa ba. Maimakon haka ya ce, “Bari Ubangiji ya tsauta maka!''
10 Amma waddannan mutane suna kawo batanci game da dukan abin da ba su gane ba. Wadannan mutane masu halin dabbobi ne, suna kwa jawo wa kansu hallaka kenan.
11 Kaiton su! Domin sun bi hanyar Kayinu, kuma sun tsunduma cikin kuskuren Bal'amu domin samun riba. Suka hallaka cikin husuma irin ta Kora.
12 Wadannan hatsari ne a boye cikin bukukuwan ku na kauna. Suna shagali ba kunya ba tsoro, suna ciyar da kansu kadai. Su holokon hadari ne marar ruwa, wanda iska ke korar sa. Su itatuwa ne shirim ba yaya, mattatu ribi biyu, tumbukakku tun daga saiwa.
13 Su rakuman teku ne masu hauka, suna fahariya cikin kumfar kunyar su. Su kamar taurari ne masu tartsatsi. Wadanda aka tanada wa duhu baki kirin na har abada.
14 Ahnuhu, mutum na bakwai daga Adamu, ya yi anabci game da su cewa, “Duba, Ubangiji zai zo da tsarkakan sa dubun dubbai.
15 Domin ya zartar da hukunci a kan dukan kowa, ya kuma cakune dukan marasa da'a a cikin dukan ayyukan su na rashin da'a wanda suka aikata a hanyar da bata cancanta ba, da kuma kalmomi masu kaifi da masu zunubi suka fada game da shi.”
16 Wadannan masu cecekuce ne, masu gunaguni, wadanda ke bin sha'awar su ta mugunta, masu tinkaho da fahariya, masu bambadanci domin ribar kansu.
17 Amma ku, kaunatattu, ku tuna da kalmomin da manzannin Yesu Almasihunmu suka gaya maku tun da.
18 Sun ce maku, “A cikin kwanaki na karshe, za a samu masu ba'a, wadanda ke bin sha'awoyin su na rashin ibada,”
19 Wadannan mutane masu haddasa tsatsaguwa ne, kuma su yan duniya ne, ba su kuma da Ruhu.
20 Amma ku, kaunatattu, ku gina kanku a cikin mafificiyar bangaskiyar ku mai daraja, kuma kuna addu'a a cikin Ruhu Mai Tsarki.
21 Ku rike kanku a cikin kaunar Allah, kuna kuma jiran jinkan Ubangijinmu Yesu Almasihu wanda ke kawo rai na har abada.
22 Ku nuna jinkai ga masu shakku. Ceci wadansu ta wurin fizge su daga wuta.
23 Ga wadansu kuma ku nuna jinkai da rawar jiki, kuyi kyamar koda tufafin jikinsu ma.
24 Yanzu, zuwa ga wanda yake da iko ya hana ku tuntube, ya kuma sa ku tsaya a gaban madaukakiyar kasancewarsa, marasa abin zargi da kuma murna mai yawa,
25 zuwa ga Allah makadaici mai ceton mu ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu, daukaka, da girma, da mulki, da iko su kasance, kamin dukan lokuta, yanzu, da har abada. Amin.