8
Da Yesu ya sauko daga dutsen, sai taro masu yawa suka bi shi. Sai wani kuturu ya zo gunsa ya yi masa sujada, ya ce, “Ubangiji, in dai ka yarda, za ka iya tsarkake ni.” Yesu ya mika hannunsa ya taba shi, ya ce, “Na yarda, ka tsarkaka.” Nan da nan aka tsarkake shi daga kuturtarsa. Yesu ya ce masa, 'Ka tabbata, ba ka gaya wa kowa komai ba. Sai dai ka je ka nuna kan ka ga firist, ka kuma bayar da baiko da Musa ya umarta domin shaida garesu? Da Yesu ya shiga kafarnahum, sai wani hafsa ya zo gunsa ya roke shi, Ya ce, Ubangiji, bawana na kwance shanyayye a gida, yana shan azaba kwarai.” Yesu ya ce masa, “Zan zo in warkar da shi.” Sai hafsan, ya ce, “Ubangiji, ban isa har ka zo gida na ba, amma sai ka yi magana kawai, bawana kuwa zai warke. Domin ni ma ina karkashin ikon wani ne, ina kuma da sojoji a karkashina, sai in ce wa wannan, 'je ka,' sai ya je, wani kuma in ce masa, 'zo,' sai ya zo, in ce wa bawa na, 'yi abu kaza,' sai ya yi,” 10 Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce wa mabiyansa, “Gaskiya, ina gaya maku, ko a cikin isra'ila ban taba samun bangaskiya mai karfi irin wannan ba. 11 Na gaya maku, da yawa za su zo daga gabas da yamma, su zauna cin abinci tare da Ibrahim da Ishaku, da Yakubu a cikin mulkin sama. 12 Amma 'ya'yan mulkin kuwa sai a jefa su cikin matsanancin duhu. Can za su yi kuka da cizon hakora.” 13 Yesu ya ce wa hafsan, “Je ka! Bari ya zamar maka gwargwadon bangaskiyar da ka yi,” A daidai wannan sa'a bawansa ya warke. 14 Da Yesu ya shiga gidan Btrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance da zazzabi. 15 Yesu ya taba hannunta, zazzabin ya sake ta, ta kuma tashi ta fara yi masa hidima. 16 Da maraice ya yi, sai mutanen suka kakkawo wa Yesu masu aljanu da yawa. Da magana kawai ya fitar da aljanun, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya. 17 Ta haka kuwa maganar annabi Ishaya ta samu cika cewa, “Shi da kansa ya debe rashin lafiyar mu, ya dauke cututtukan mu.” 18 Sa'adda Yesu ya ga taro masu yawa kewaye da shi, sai ya ba da umarni su tafi su koma wancan hayi na tekun Galili. 19 Sai wani marubuci ya zo ya ce masa, “Malam, zan bi ka duk inda za ka je.” 20 Yesu ya ce masa, “Yanyawa suna da ramukansu, tsuntsayen sama kuma da shekunan su, amma Dan mutum ba shi da wurin da zai kwanta.” 21 Wani cikin almajiran ya ce masa, “Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne mahaifina.” 22 Amma Yesu ya ce masa, “Bari matattu su binne matattunsu.” 23 Da Yesu ya shiga jirgi, almajiransa suka bi shi. 24 Sai ga wata babbar iska ta taso a tekun, har rakuman ruwa suka fara shan kan jirgin. Amma Yesu yana barci. 25 Sai almajiran sa suka je suka tashe shi, suka ce, “Ubangiji, ka cece mu, za mu hallaka!” 26 Yesu ya ce masu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu karancin bangaskiya?” Sa'annan ya tashi, ya tsauta wa iskar da tekun. Sai wurin gaba daya ya yi tsit. 27 Mutanen suka yi al'ajibi, suka ce, “Wanne irin mutum ne wannan, wanda har iska da teku ma suke masa biyayya?”. 28 Da Yesu ya zo daga wancan hayin a kasar Garasinawa, mutane biyu masu al'janu suka fito suka same shi. Suna fitowa daga makabarta kuma suna da fada sosai, har ma ba mai iya bin ta wannan hanya. 29 Sai suka kwala ihu suka ce, “Ina ruwanka da mu, kai dan Allah? Ka zo nan ne ka yi mana azaba tun kafin lokaci ya yi?” 30 To akwai wani garken aladu masu yawa na kiwo, babu nisa da su. 31 Sai al'janun suka roki Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.” 32 “Yesu ya ce masu, “To, ku je.” Sai aljanun suka fita, suka shiga cikin aladun. Sai kuwa duk garken suka rugungunta ta gangaren, suka fada cikin tekun, suka hallaka a ruwa. 33 Mutanen masu kiwon aladun suka gudu, suka shiga gari, suka yi ta ba da labarin komai da komai, musamman abin da ya faru da masu al'janun. 34 Sai duk jama'ar gari suka fito su sami Yesu. Da suka gan shi, suka roke shi ya bar kasarsu.