20
1 Sai na ga mala'ika na saukowa daga sama. Yana da makullin rami marar iyaka, yana kuma da babar sarka a hannunsa.
2 Sai ya dauki tsohon macijin, wanda shine iblis, ko shaidan, ya daure shi shekaru dubu.
3 Ya jefa shi cikin rami marar iyaka, ya rufe shi ya kuma sa hatimi a bisansa. Hakan ya faru ne domin kada ya kara yaudarar al'ummai har sai bayan shekaru dubu. Bayan wannan, dole a sake shi na dan lokaci.
4 Sa'annan na ga kursiyoyi. Wadanda ke zaune a bisansu sune wadanda aka ba ikon hukunci. Na kuma ga rayukan wadanda aka fille wa kai saboda shaidar Yesu da maganar Allah. Ba su yi wa dabban sujada ba ko siffarsa, suka ki su karbi alamar a goshinsu ko a hannu. Sun sake rayuwa, suka yi mulki tare da Kristi shekaru dubu.
5 Sauran matattun basu sake dawowa da rai ba har sai da shekaru dubu din suka cika. Wannan shine tashin matattu na fari.
6 Mai albarka ne mai tsarki ne kuma wanda yake da rabo cikin tashin matattu na fari! Mutuwa ta biyu ba ta da iko akan wadannan. Za su zama firistocin Allah da na Almasihu za su kuma yi mulki tare da shi shekaru dubu.
7 Sa'adda shekaru dubu suka zo ga karshe, za a saki shaidan daga kurkukunsa.
8 Za ya fito domin ya yaudari al'ummai da ke kursuyoyi hudu na duniya, Gog da Magog ya tattara su domin yaki. Yawan su zai zama kamar yashin teku.
9 Suka bazu a fuskar duniya suka kuma kewaye sansanin masu ba da gaskiya, kaunataccen birni. Amma wuta ta sauko daga sama ta lankwame su.
10 Shaidan, wanda ya yaudare su, aka jefa shi cikin korama ta farin wuta mai ci, inda aka jefa dabban da makaryacin annabin. Za su sha azaba dare da rana har abada abadin.
11 Sai na ga babban kursiyi da wanda ke zaune a kansa. Duniya da sama suka guje wa fuskarsa, amma babu wurin da za su tafi.
12 Na ga matattu manya da kanana- suna tsaye gaban kursiyin, aka bude litattafai. Sai aka bude wani littafi - Littafin rai. Aka yi wa matattu shari'a bisa ga abinda aka rubuta cikin litattafan, gwargwadon ayyukansu.
13 Teku ta ba da matattun dake cikinta. Mutuwa da hades suka ba da matattun da ke cikinsu, aka yi masu shari'a gwargwadon abin da suka yi.
14 Aka jefa mutuwa da hades cikin tafkin wuta. Wannan shine mutuwa ta biyu - tafkin wuta.
15 Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce cikin littafin rai ba, aka jefar da shi cikin tafkin wuta.