2
1 Amma kai, ka fadi abinda yayi daidai da amintaccen umarni.
2 Dole tsofaffin mazaje su zama masu kamun kai, masu daraja kansu, masu-hankali, masu aminci cikin bangaskiya, cikin kauna da jurewa.
3 Haka ma tsofaffin mataye su kame kansu da girma, ba magulmata ba. Kada su zama bayi wajen yawan shan ruwan inabi. Su koyar da abubuwa masu kyau
4 domin su koyar da kananan mataye da hikima su kaunaci mazajensu da 'ya'yansu.
5 Su horar dasu su zama masu hikima da tsabtar zuci, masu tsaron gidajensu, kuma masu biyayya da mazajensu. Suyi wadannan abubuwa saboda kada maganar Allah ta sami zargi.
6 Ta haka kuma, ka karfafa samari, su zama masu hankali.
7 A kowanne fanni, ka mayar da kan ka abin koyi a cikin kyawawan ayyuka; idan kayi koyarwa, ka nuna mutunci da martaba.
8 Ka bada sako lafiyayye marar abin zargi, yadda masu hamayya da maganar Allah zasu ji kunya, domin rashin samun mugun abin fadi akan mu.
9 Bayi suyi biyayya ga iyayengijin su a cikin komai. Su faranta masu rai, ba suyi gardama dasu ba.
10 Kada suyi sata. Maimakon haka, sai su nuna dukan bangaskiya mai kyau, domin suyi wa koyarwarmu game da Allah mai cetonmu kwalliya a cikin dukan komai.
11 Domin alherin Allah ya bayyana ga dukan mutane.
12 Yana koya mana mu musanci miyagun ayyuka, da sha'awoyin duniya. Yana horar damu muyi zama cikin hankali, da adalci a cikin hanyar allahntaka a wannan zamani
13 yayin da muke cigaba da jiran karba albarkataccen begenmu, wato bayyanuwar daukakar Ubangiji Allah da kuma mai cetonmu Yesu Almasihu.
14 Yesu ya bada kansa domin mu, domin ya cece mu daga rashin kiyaye doka ya mai damu masu tsarki, domin sa, mutane na musamman wadanda suke da marmarin aikata kyawawan ayyuka.
15 Ka yi magana da karfi ka karfafawa wadannan abubuwa. Ka yi gyara da dukan iko. Kada ka bar wani ya raina ka.